(ABNA24.com) Gabanin tashinsa daga filin saukar jiragen sama na Tehran, Ali Riza Rashidyan ya fadawa manema labaru cewa ziyarar tashi tana da alaka ne da gayyatar da mahukuntan Saudiyya su ka yi masa.
Ali Riza Rashdiyan ya kuma kara da cewa; Muna fatan cimma matsaya da mahukuntan Saudiyyar dangane da yadda al’ummar Iran za su gudanar da aikin Haji na shekara mai zuwa cikin muutnci da daukaka.
Har ila yau shugaban hukumar aikin haji da ziyarar na Iran ya kuma yi ishara da adadin mutanen Iran da su ka yi rijistar aikin haji na shekara mai zuwa tare da nuna fatansa na ganin cewa an kara yawan kason da za a bai wa Iran a aikin hajin bana.
/129